Friday, 14 October 2016

*MUHIMMAN CHIN TIRAREN MISKI GA DAN ADAM*

Daga Zauren
Khulafa'ur-rashiidun.
:
*Shidai miski turarene me "Kamshi"kamshin kuma maisa nishadi da annashuwa.*
;
*Yanada kyau kwarai da gaske ace amatsayinki na mace koda yaushe yakasance kinada miski adakinki domin anaso koyaushe kirinka amfani dashi.*
*
Mun riga munsani shi kamshi abune dayake kara dankon soyayya kuma yake dawwamar da ita,sannan miski yana dauke da sinadarai dadama dasuke bawa farjin mace kariya daga cututtuka,saboda haka anaso kullum mace tarinka amfani dashi.
:
Kalolinshi guda uku 3⃣ ne.
akwai fari mekamar madara me kauri:
shi wannan ba'a sashi acikin farji saboda adaskare yake bai fiya narkewa ba,sai dai ashafashi daga wajen farji.
:
Akwai fari kal kamar ruwa kamshinsa kusan dayane da mekaurin sai dai shi bashida kauri,to shi za'a iya "inserting"(matsi)dashi tabbas yana taimakawa har a6angaren auratayya kuma duk sanda mijinki yaji wannan kamshin ko bakwa tare ta zai tunaki Zaiyi sauri_sauri ya dawo gida kinga miski yayi amfani kenan.
:
Akwai jan miski wannan masu fama da matsalan aljanu suke shafashi domin yana fatattakar aljanu da iznin ALLAH
:
Abinda nasani dai idan me aljanu tana shafashi indan anriga ammata rukiyya ta suna rabuwa da ita
Amma idan ba ayiba to zakaga batasan kamshinsa baza tayi amfani dashiba
;
Shi ana shafashine aduk jiki da ga6ar da tafiyiwa me fama da aljanun ciwo
:
Kunsan fa miski asali yadauko yanada kyau kiyi taka tsantsan gurin amfani dashi domin bawai kawai dangwala zakiyi da yatsanki kisakaba a'a,
:
Zaki nemi ruwan dumine bamai zafi sosaiba kije ki kama ruwa dashi ki wanke gurin sosai, sannan kisami handkerchief mekyau ki goge ko da tissue, daganan saiki sami *"cotton bud"* wato abin sosa kunne
:
Sai ki dangwalo dashi sannan kiturashi agabanki kidan matse kafarki sai kicire ki yar.
to wallahi ko fant dinki kika cire kamshi zakiji baZeyi wari ba.
:
Babu kunya cikin neman ilmi musamman ilmin addini babban abun kunya ace mijinki zai kusanceki kuma yaji farjinki yana wari haba wannan ai ba aji.
:
Zaki iya dafa ganyen magarya inya huce kizuba miskin kina kama ruwa dashi.
:
Sannan anaso duk sanda zaki saka pant dinki to ki diga miskin akai duk wasu kwayoyin cuta zasu mutu da yardar Allah.
:
Ana kuma shafa miski ajiki ana kuma hadashi acikin Humra yana kuma taimakawa macen data haihu kwarai da gaske.
:
Yanada kyau ace amatsayinki na mace kar arasaki da wadannaabubuwan👉🏻
:
🍭MISKI
🍭GANYEN MGARYA
🍭HULBA
🍭HABBATUSSAUDA
🍭MAN ZAITUN
🍭MAN TAFARNUWA
🍭KHALTUFA
🍭LALLE
🍭ZUMA
:
Bara na takaita haka 'yan uwa.   Haza ma'indii wabillahittaufik.

2 comments: