11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar magani suke, akai akai ake bukatarsu. Wasu kuma kamar abinci suke, a kullum dole ne a neme su. Yi kokari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa.
12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne o Mala’ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka!
13. Ana yin da-na-sani ne a kan Magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba. Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin Magana ba.
14. Kada ka damu da masu kulla ma ka sharri, duk iya kokarinsu bas u wuce zartar da kaddarar Allah akan ka.
15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne:
*Fadin Gaskiya
* Cika Alkawari
* Rikon Amana
* Jin Tausayi da
* Kyautata ma mutane
Rubutawa Dr. Mansur Ibrahim Sokoto
No comments:
Post a Comment