Sunday, 30 October 2016

🌍HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN). 🌍

ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA: 🌍

“Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.

Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.

Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.

Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.

Ya ku jama'a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.

Ku tuna fa(ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.

Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.


YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!

 Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin MuhammadMuhammad (saw) ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍

No comments:

Post a Comment