Sunday, 25 September 2016

*BANDA SON KAI*

*cikin mutanennan wa yafi shirme da rashin kan gado?*

*1- BAKANO:* Wanda yana likita ya tada wani maras lafiya daga Bacci musamman domin yayi masa allurar Bacci.

*2- BASAKKWACE:* Wanda yake yiwa shuka ban-ruwa a dai-dai lokacin da ake sharara ruwan sama

*3- DAN FILANI:* Daya fesa turare a jikinsa a dai-dai lokacin daukar hoto da niyyar wai idan an wanko hoton zaiji kamshin turaren.

*4- DAN-KADUNA:* Daya sanya radio a Firij domin ya saurari COOL MUSIC.

*5- DAN-KEBBI:* Wanda yaci abinci a Hotal ya wanke kwano.

*6- BABARBARE:* Wanda yaga tsugunna ya gaida sarkin garinsu lokacin daya ganshi a TV a wajan wani taro.

*7- DAN-BAUCHI:* Wanda yasa aka yi masa polish a takalmi saboda zaiyi hoton passport

*8- BAKATSTSINE:* Wanda yana tafiya yayi tuntibe da wani abu a duhu saiya dauka ya shinshina yaji ashe kashi ne sai yace Allahamdullah da ban taka ba.

*9- DAN-GASHUA:* Wanda ya yaje Banki da sifana zai bude acount

*10- BAZAMFARE:* Wanda yayiwa ATM CARD dinsa Laminashin saboda gudun karya karye/kode

*Banda son kai...*

No comments:

Post a Comment