Friday, 30 September 2016

Gwaji so

Wata mata ce tanason ta gwada mijinta; Taga inhar suka rabu yaya zaiyi?... Saita dauki takarda tayi rubutu kaman haka; "mijina gaskiya bana sonka yanzu jinake na tsaneka bana bukatar kallon fuskanka gara na kalli fuskan goggon biri da na kalli fuskan ka, bana burin jin muryanka gara na saurayi wakar shata da naji muryanka, dan haka nayi tafiyata ka auro wata....... Sai ta ajiye akan kujeran da yake falon sannan takoma bayan kujeran ta buya... Mijinta yana zuwa yasamu bakowa a falon yana kokarin zai kirata sai yaga takarda akan kujera, sai yadauka yakaranta... Nan take ya fashe da dariya sannan ya dauko wayansa yasa akunnensa yafara cewa, Hello masoyiyata abunda muka dade muna addu'ar shi yau yazo. Yanzu nadawo daga wajen aiki na samu wannan lalatacciyar matan nawa tabar gidana kinga sati mai zuwa kawai sai adaura mana aure... Sai ya fashe da dariya yace kijirani yanzu ina zuwa zamu tafi hotel muci abinci..... Bayan yagama maganganunsa sai yajuya bayan takardar yayi rubutu sannan ya bude durowa ya canja riga ya fita yana waka wannan baitin....SOYYAYYA SO MAI SONKA... ZO MUJE MUJEJEJE MUJE MUJE....Haka ya fita yana wakarsa fuskansa cike da annuri. Fitarsa keda wuya matar tafito tana ta kuka tadauki takardan dan ganin meya rubuta.... Sai taga yarubuta.....;Kidaina boye-boye Kifito dan nariga na ganki abayan kujera, kidafamun ruwan tea yunwa nakeji, naje insayo biredi. Wai a Cikinsu wa akafi razanawa? 1=Matar....?? 2=Mijin.....??

No comments:

Post a Comment