Sunday, 25 September 2016

*KUJI TSORON ALLAH, KUYI ADALCI A TSAKANIN 'YA'YAN KU!*

بسم الله الر حمن الر حيم
Fara  karatun littafin

*HAQQUN MUBIIN* wallafar- malam kabir Abdullahi muhammad Al-kanawi.

 fitowa na 004

Daga zauren.

*KHULAFA'UR-RASHIDUN.*

HADISI NA 004

عن نعما بن بشير-رصي الله عن-قال:قال رسول الله-(ﷺ)"اتقو الله, واعدلو في اولادكم"   رواه ابجاري و مسلم.

An nu'umani ibn bashir radillahu anhu Qala: Qala: rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam "ittaqullaha wa'Adiluu fii Awladikum"

Rawahul bukhari wa muslim.

Ankarbo daga nu'umani dan bashir ALLAH yaqara masa yadda yace, manzon ALLAH tsira da aminci su tabbata a gare shi yace "kuji tsoron ALLAH, kuyi Adalci a tsakanin yaranku"

*FA'IDA*

Kaji tsoron ALLAH iyaka matuqar jin tsoron ALLAH, kada ka fifita  'yayan amarya akan na uwar gida kada ka fifita wasu sama da wasu, saiwanda ya fisu tsoron ALLAH.  Kana da daman da zaka sa wanda yafi kowanne hazaqa a makaranta mai tsada ta yadda inksashi bazai ma asaran kudin makaranta ba, sabda zuciyan shi tana haddace abubuwa dayawa.

Amma zakasamu dayawa a yanxu,  mutu yanda 'ya'ya  amma bazai ware wayafi hazaqa ba sai a dauki dan amarya  ko dan uwar gida da ake ji dashi. Ire iren hakan kuskur ne.

Sanan bai halatta ka ke6angi danka da babban kyauta batare da ka bama sauran ba.
Idan ka sayar mar mota, sannan yanada Qanwa mace ita ma kasaya mata mota ko abinda yake dai dai da motan, komai dai dai wa dai da. Tinda ba rabon gado bane balle a fifita na miji a bar mace.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::
_Daga  dan uwan ku a musulunci._
MUHAMMAD AUWAL ABU JA'AFAR AL-POTISKUMAWI.
17-11-1437A.H 20-08-2016
---------------------------------
→ MasU buqatan kasan cewa damu a whatsapp.
+2347035269582
+2348063796175
 tare da cikakken suna da kuma cikakkiyar sallama. don samun karatuttukan mu a facebook, saikubi, mobile.facebook.com/Khulafaur-Rashiidun-1812718708973541/ Subhanak Allahumma wabi hamdika Nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka
Wana tubu ilaik.

No comments:

Post a Comment