Sunday, 25 September 2016

DUNIYAR KWANA UKU CE 👌

💧JIYA:- Ta tsere maka da dukkan abunda yake cikinta sai abunda ka aikata shi don Allah kana me neman yardar Allah da shi.

💧GOBE:- Ta yi maka nisa, ba lalle a wayi gari da kai ba kamar yadda Annabi S.a.w Yake cewa Mu Irga kawunan mu cikin Matattu. (ma'ana mu sakankance da cewar bazamu kai gobe ba).

💧YAU:- ITA CE TAKA.
'Dan uwana & 'Yar'uwata YAU ita ce mafi tsadar ranaku a cikin Ranakunmu na Duniya, Domin Jiya ta wuce, kuma bamu da tabbas akan gobe.

👉 Don Haka Mu Nesanci Ayyukan Sabo YAU ba sai GOBE ba. Mu Kusanci Kyawawan Ayyuka YAU ba sai GOBE ba.

🙏 Allah Ya Datar Damu Da Aikata Abunda Aka Horemu Da Aikatawa.

🙏 Allah Ya Tsaremu Daga Aikata Abunda Aka Hanemu.

Zauren Minbarin Malaman Sunna (whatsapp)

+2347061908607
Ishaq Danso Azare.

No comments:

Post a Comment