Sunday, 25 September 2016
*DAUSAYIN SHIRIYA 31*
Yana daga cikin addu'ar Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama: *اللهم اغفر لي ذنبي و وسع لي في داري و بارك لي في رزقي* *_Allahummag firliy zanbiy, wa wassi'liy fiy daariy wa baarikliy fiy rizqiy_* Ma'ana: Yaa Allah ka gafarta mun zunubaina, Ka yalwata mun a gidana, Kuma Ka yi mun albarka a cikin arzikina. A duba littafin Sahihul Jaami'. Kuma Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani ya ce hadisi ne Hasan. Mu haɗu a fitowa ta 32 in sha Allahu Ta'ala. ✍🏼 Dan uwanku a Musulunci: *_Umar Shehu Zaria_* [13:53, 04/09/2016] 🌹💍🌹: *DAUSAYIN SHIRIYA 32* Umar Bn Khaddab, Allah Ta'ala Ya kara yarda a gare shi, ya na cewa: *_"Dukkan wanda yake so dan uwansa Musulmi ya so shi: Ka fara yi masa sallama idan ka hadu da shi, sannan ka kira da mafi soyuwan suna a gare shi, kuma ka yalwata masa wurin zama idan zai zauna tare da kai"_* Mu haɗu a fitowa ta 33 in sha Allahu Ta'ala. ✍🏼 Dan uwanku a Musulunci: *_Umar Shehu Zaria_* [13:53, 04/09/2016] 🌹💍🌹: *DAUSAYIN SHIRIYA 33* Kananan dabbobi sun kasance tsahon rayuwarsu su na tsoron kada kyarkeci ya cinye su, amma a ƙarshe sai a wayi gari mai kiwon su ne yake cinye su. Don haka, kai ma a rayuwarka kar ka ji tsoron kowa sai Allah kuma ka bar duk wani abu da zai same ka nan gaba a hannun Allah. Mu haɗu a fitowa ta 34 in sha Allahu Ta'ala. ✍🏼 Dan uwanku a Musulunci: *_Umar Shehu Zaria_* [13:53, 04/09/2016] 🌹💍🌹: *DAUSAYIN SHIRIYA 34* Idan kana so ka gane irin mu'amalar da 'ya'yanka za su yi maka a lokacin da ka tsufa ko ka mutu, to ka duba yanda kake mu'amalantar iyayenka a lokacin da suke raye ko bayan sun mutu, domin rayuwa kamar madubi ne yanda ka kalleta, ita a haka zata kalle ka. Mu haɗu a fitowa ta 35 in sha Allahu Ta'ala. ✍🏼 Dan uwanku a Musulunci: *_Umar Shehu Zaria_*
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment