*MU KOMA KITCHEN*🍹🍷🍗🍴🍔😋
*BIRTHDAY CAKE*
*Ingredients*
_Flour_
_Egg_
_Sugar_
_Butter_
_Backing powder_
_Icing sugar_
*Method*
_Zaki samu sugar da butter ki hadasu wuri daya kita murzasu har sai koma ruwa ruwa saiki zuba kwai aciki kici gaba da murzawa yadda zasu hade sosae saiki zuba backing powder aciki flour ki juya su su hade sosae saiki dinga dinar garin flour kina zubawa cikin kwan nan da butter wanda ki ka murza kina zubawa kina nurzawa har sai kinga ya hade amma fa kwabin kada yayi tauri abin lura kuma shine idan kika fara murzawa da hannun dama to kici gaba da murzashi da dama din har sai kin gama._
_Idan ma da hannun haggune haka zakiyi dashi din har sai kin gama,domin da kin canja to zai warware, idan kin gama saiki zuba cikin gwangwayen nan na birthday cake kuma kafin ki zuwa saiki shafama gwangwanayen butter saiki gasa bayan kin gasa cake din saiki fiddo shi ya huce saiki shafe shi da jam amma ki kware saman cake din kafin ki shafa jam din saiki dauko icing sugar da farin ruwan kwai banda gwaiduwar saiki sa kalar da kikeso,zaki fasa kwai saiki kwashe gwaiduwar ki aje agefe saiki hade icing sugar da farin ruwan kan saiki bugashi ya bugu sosae yayi tauri kamar yadda ake kwaba cincin saiki sanyashi kan faranti ki murza shi sosae kamar yadda ake murza cincin saiki daura cake din daidai inda kika shafama jam din idan kin daura zakiga ya manne ajikin cake din._
_Zaki iya yin duk irin kwalliyar da kikeso da kuma rubutu idan kina da icing sugar da ruwan kwai da dukkan nau'in kalar da kikeso.
No comments:
Post a Comment