Sunday, 25 September 2016

Musiba guda biyu da suke samun kowane mutum a lokacin mutuwar shi, su ne:

[21:39, 31/08/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 35*

*_Za a kwashe dukkan dukiyansa, domin ba za a rufe shi da su a kabari ba sun zama na magada_*

*_Sannan ranar alkiyama za a tambaye ka game da yanda ka samu dukiyar_*

Don haka mai hankali shi ne wanda yake taimakon addini da dukiyarsa.

Mu haɗu a fitowa ta 36 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
[19:42, 01/09/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 36*

Kar ka yarda shaidan ya sanya maka kiyayya ko keta akan wani dan uwanka musulmi, domin matukar ka bari daya daga cikin wadannan ya shiga zuciyarka, to daga nan zaka iya kamuwa da cutar hassada, wanda ba zata taba barin ka, ka yi sukuni ba, kullum kana cikin baƙin ciki.

Mu haɗu a fitowa ta 37 in sha Allahu Ta'ala

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
[23:38, 02/09/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 37*

Kullum ka tabbata ka bude ranarka da sallan asubahi akan lokaci da yin azkar na safiya wanda Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya koyar, domin su ne hanyan tsira da rabauta kuma babu mamaki wannan ita ce safiyarka ta karshe a duniya.

Mu haɗu a fitowa ta 38 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
[22:55, 03/09/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 38*

Allah Ta'ala Ya halicci dan Adam mai rauni wannan ya sanya muke zunubai, don haka ka lizimci tuba da istighfari koda yaushe, domin su ne suke kankare zunubai.

Mu haɗu a fitowa ta 39 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
[23:17, 04/09/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 39*

Komai Allah Ta'ala Ya kaddara Yanda yake so ya kasance, kuma babu wanda zai iya canja kaddaran Allah.

Don haka, kar ka daina rokon Allah (addu'a), domin ita ce igiyar tsira.

Mu haɗu a fitowa ta 40 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
[22:39, 05/09/2016] ‪+234 813 762 7053‬: *DAUSAYIN SHIRIYA 40*

Mai hankali shi ne wanda yake tunani kafin ya fadi magana, domin ya san Mala'iku suna nan suna rubuta duk abun da ya furta, kuma za a bijiro masa da su ranar alkiyama a yi masa hisabi akan abun da ya fada.

Don haka, mu kiyaye harshenmu.

Mu haɗu a fitowa ta 41 in sha Allahu Ta'ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*

No comments:

Post a Comment