Sunday, 25 September 2016

*TAQAICECCEN TARHIN KHALIFA NA FARKO A MUSULUNCI* fitowa na 02

Daga Zauren
*KHULAFA'UR-RASHIIDUN* WhastApp.

*بسم الله الر حمن الر حيم*


    🔘GABATARWA🔘
Na rubutashi da tsawo sabada in ana karanta tarihi musammam na manayan bayiN ALLAH saikaji dadi bazaka so ka daina karantawa ba.
Zan cire  karatuttukan ne kusan gabadaya daga littai Qaddara ta riga fata. na  DR. MANSUR IBRAHIM SOKKOTO.
🕋
*1.6 MATSAYINSA KAFIN ZUWAN MUSULUNCI*

Abubakar yayi fice a zamanin jahilaya da ilmin da ake kira Ansab, sanin dangantakar mutane da tarihin sanin gidajensu da abuuwan arzii ko rashin arzikin da suka gudun a tsaksnin mutane ko tsaknin Qabilu.
Sannan kuma shine wakilin reshrn gidan su a majalisan zartar wa na Quraishawa wadda ta hafa da rassa goma na wannan Qabilar, ko waneene gida da aikin sa da wanda yake wakiltarsa.  gasu kaman haka

1-Banu hashim, 2 banu umayya. 3- banu naufal. 4 banu Abdid dar. 5 banu Asad. 6 Banu taim. 7 banu makhzum. 8 Banu adyyin. 9 Banu juma. 10 banu sahm.

1- BANU HASHIM. suke kula da shayar da alhazai ruwa. wakilinsu a majalisan  shine Abbas dan Abdul mudallabi, baffan manzon ALLAH (ﷺ), wannan office inbya chigaba da aiki bayan zuwan musulunci.

2-Banu umayya:  suke riqe tutar Quraishawa, kuma suke rikon kwarya duk lokacin da aka rasa shugaba  kafin a hadu akan sabon da za'a nada. Wakilin su a majalisan  shine ABU SUFYAN DAN HARB.

3-BANU NAUFAL: Suke kula da asusun tallafi na taimakon alhazai da guzuri ya yanke musu. Wakilinsu shine Al-haris dan amir.

4- BANU ABDI DAR-  suke kula da wanke ka'aba da tufataar da ita. Wakilinsu shine USMAN DAN DALHA.
5-BANU ASAD:  suke da ofishin sakatariya. Duk shawarar da aka yanke suke sa mata hannu kafin a aiwatar da ita.  Wakilinsu shine  YAZID DAN ZAM'AH DAN ASWAD.

6-BANU TAIM- suke da alhakin hada kudi don biyan diyyya idan aka sasanta masu fada da kuma biyan bashi idan wani baQuraishe ya kasa. Wakilinsu shine ABUBAKAR DAN KUHAFA.
7-BANU MAKHZUM-suke kula da wajen ajjiye makamai. Wakilinsu  KHALID BIN WALID.

8- BANU ADIYYIN- sune masu kula da huldar Quraishawa da saura  Qabilu, musammam wajen  sha'anin yaki da zaman lapiya. Kuma suke da alhakin shelanta darajojin  Qabilar su don tayikwarjini  a idon sauran mutane, wakilinsu shinr UMAR DAN KHANDAB.

9-BANU JUMAH: suke kula da kuri'a da ake yi don neman sa'a in za ayi tafiya ko cinik koAure ko makamancin su. wakilinsu shine SAFWAN DAN UMAYYA.

10- BANU SAHM:  suke kuka da tattalin arzikin da abinda ya shafi gumaka.
A-HARIS DAN KASIS.

*1.4 MUSULUN TAR SA*

masana tarihi sun rawaito cewa, tin kafin wahayi ya fara sauqa ga manzon ALLAH (ﷺ), ABUBAKAR  yayi wani mafarki wanda ya labarta shi ga babban malamin nan masanin addinin Nasara da ake cema sa  BAHIRAH. Sai ya tambaye shi daga ina ka fito? yace masa daga makka. Yace, minene sana'ar ka? yace  fatauci. BAHIRA yace, idan ALLAH ya gaskata mafarkin ka to, wani mano zai bayyana daga cikin jama'arka , zaka taimaka masa a rayuwar sa, kuma ka wakilce shi bayan mutuwar sa.
( _Inama nine nayi wannan mafarki wato ni muhammad auwal abuja,afar_)

                             Awata tafiya kuma kuma da yayi zuwa qasar Yaman ya samu bushara  mai kama da wannan daga wurin wani malami daga Qabilar Azd.

         A lokacin da ALLAH madaukakin sarki ya aiko manzon sa, Abubakar baiyi wata-wata ba ya bada gaskata shi yana mai cewa, bamu ta6a gwada qarya a kanka ba, kuma ka cananci manzanci saboda tsoron amanr ka da sada zumuncim ka da kyakkyawar zaman takewarka da jama,a. Daganan Abubakar yaciga da zama na hannun daan manzom ALLAH(ﷺ) har inda mai raba masoya ta rabasu (MUTUWA).


*1.5 GUDUMAWAR SA GA ADDINI*

Kasancewar sa mai arziki kuma dattijo, kuma na hannun daman manzon ALLAH (ﷺ) ya bashi damar taimakawa  ma addinin musulunci ta hanyoyi da dama; a Makka ya kasance me bada karia a manzon ALLAH(ﷺ), daga musgunawa da cin zarafi da mushirikai suke masa.

Har ALI DAN ABU DALIB yake cewa, bayan Mutuwae  ABU DALIB babu wanda yake wa kafurai tinkanzir idan suna musguna ma  manzon ALLAH (ﷺ) sai Abu-bakar.
Ga kuma dukiyar sa day bayar wajen ci gaban addini har manzom ALLAH (ﷺ) yake cewa "Dukiyar kowa bata amfa neni ba kamar yadda dukiuar Abuba ta ta amfane ni".

Abubakar ya taya manzon ALLAH (ﷺ) WAJEN kiran mutane zuwa ga musulunci inda ya janyo musuluntar dukkan maqarraban sa da  amintattunsa kamar su _Usman dan affan, da zubairu dan awwam da dalhatu dan ubaidullah da   Abdurahaman dan Auf da sa'aduDan abu waqas_  wadanda  dukkansu suna cikin mutane goma da ALLAH da manzon ALLAH(ﷺ), yayimu bushara  da aljannah.

Sannan da gabisani ya musuluntar da usamanu dan Muz'un da amiru (Abu Ubaidah) dan jarrah, da ArQamu dan  Abul- ArQam da Abu salamata Al makhzumi wadanda sune magabatan farko a shiga  musulunci.  cikin wadan ya jawo su musuni hadda mahaifinshi.

                      🕋******🕋
LAIIPIN DADI QAREWA!!! WATO IDAN KANA SAURA RON TARIHIN MUTNANAN KIRKI MUSAMMAM WADAN NAN WANDA AKA MUSU ALJANNAH DA ALJANNA. Balle kaji ance ABUBAKAR SIDDIQ sekaji dadi.
Qur'ani ya ambace su ya yabesu ya basu shaida mai kyau ya kuma basu aljannah.
Duk wanda kaga yana zagin wadan tofa tabbas ya qaryata Qur'ani,  sannan bai yadda ba yanadag cikin wadanda suka Yadda an jujjuya Qur'ani idan yace ma yayada Da kur'ani ka kawomar ayyi da suka ya besu kaji mi ze ce ma.

Surah Al-Fath, Verse 29:
Bismillhir rahamanir rahim
مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَمَثَلُهُمْ فِي الْإِنجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا

shiyasa malam duk wanda kaka yanajin haushin u tofa kafuri ne!!
Kui Qoqaron fahintar dashiin  yaqi fahinta ku kyale shi.

Zan dakata anan.

No comments:

Post a Comment